Manyan 'yan siyasa 2 su na fafatawa a zagaye na 2 a zaben Nijar
A yayin da al’ummar Jamhuriyar Nijar, suka soma kada kuri'a a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa, za suyi zabi ne tsakanin manyan ‘yan siyasa masu fada a ji 2, a zaben shugaban kasa, zagaye na 2 a yau Lahadi, a kokarinsu na tabbatar da mika mulki daga hannun farar hula zuwa farar hula a karon farko a tarihin kasar da juyin mulki ya wa katutu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Daga cikin al’ummar kasar miliyan 22,miliyan 7 da dubu dari 4 ne kawai suka cancanci kada kuri’a a yaau Lahadi, sauran kuwa, ba su kai munzulin kada kuri’a ba.
Dubban sojoji ne aka girka a sassan kasar don tabbatar da tsaro a yayin kada kuri’ar a kasar da ke kan hanyar mika mulki cikin lumana tsakanin daga zababben shugaba daa wa’adinsa mulkinsa ya cika, zuwa wani zababben shugaban, a karon farko tun da kasar ta samu yancin mulkin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekarr 1960.
An yi na’am da shawarar shugaban Nijar mai barin gado, Mahamadou Issoufou na sauka daga karagar mulki, bayan cikar wa’adin mulki 2na shekaru 5 kowanne a nahiyar da shugabanni da dama suka yi kokarin yin kane kane a kan madafun iko.
Magajinsa zai kasance na hannun damarsa kuma wanda yake goyon baya, Mohamed Bazoum ko Mahamane Ousmane, wanda ya kasance zababben shugaban kasar na farko a shekarar 1993, sojoji suka hambarar da shi bayan shekaru 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu