Jam'iyyun adawa sun shirya kalubalantar sakamakon zaben Mali
Wasu 'yan takaran zaben shugaban kasar Mali da akayi a karshen mako sun bayyana aniyar su ta kalubalantar sakamakon zaben a kotu saboda abinda suka kira tafka magudi da akayi.
Wallafawa ranar:
Wani taron manema labarai da 'yan takaran suka kira cikin su harda tsohon ministan kudi Soumaila Cisse da dan kasuwa Aliou Diallo, sun bayyana cewar ba za su amince da sakamakon zaben da ake saran bayyana shi ranar juma’a ba.
Daraktan yakin neman zabem Cisse, Tiebile Drame ya ce suna da shaidar da ke nuna musu cewar akwai kauyen da ke da mutane 150 amma kuma mutane 3,000 sun kada kuri’a acan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu