Isa ga babban shafi
Mali

Al'ummar Mali sun kada kuri'a a zaben shugaban kasa.

Al'ummar Mali sun kada kuri'a a zaben shugaban kasa, wanda cikinsa akalla sama da ‘yan kasar miliyan takwas suka fita domin tantance waye zai zama gwaninsu.

yan kasar mali a kan layin rumfar zaben shugaban kasa
yan kasar mali a kan layin rumfar zaben shugaban kasa REUTERS/Luc Gnago
Talla

Zaben ya zo ne a dai dai lokacin da jami’an tsaro a kasar, ke kan kokarin kawo karshen hare-haren ‘yan ta’adda da kuma rikicin kabilanci.

Shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita, wanda ke neman wa’adi na biyu, zai fafata ne da ‘yan takara 24, ciki harda babban abokin hamayyarsa Souma’ila Cisse.

A zaben baya dai, shugaba Boubacar keita, ya samu nasarar darewa shugabancin Mali ne, bayan lashe kashi 77.6% na yawan kuri’un da aka kada.

Yayin yakin neman yin tazarce, shugaban na Mali, ya bayyana cimma sulhu da gwamnatinsa ta yi da tsaffin ‘yan tawayen Azibinawa a shekarar 2015, a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan ci gaba da ‘yan kasar ba za su manta da shi ba.

Har yanzu dai ‘yan kasar ta Mali na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, da tashe tashen hankula da suka shafi na kabilanci, daga arewaci zuwa tsakiyar kasar, duk da cewa akwai dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya akalla dubu 15, 000 a kasar, zalika ga dakarun Faransa 4,500 da kuma rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel.

A watan Nuwamba mai zuwa na 2018, dokar ta bacin da gwamnati ta ayyana a kasar za ta shiga shekara ta hudu da fara aiki, a dalilin matsalolin tsaron da ake fuskanta.

Wani rahoton majalisar dinkin ya ce daga farkon 2018 zuwa watan Yuli sama da fararen hula 300 ne suka rasa rayukansu a rikicin kabilanci kadai, mafi akasari, a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar ta Mali.

Kungiyar Fulani da ke kasar ta ce a ranar Laraba, kwanaki hudu kafin soma zaben shugabancin kasar, wasu mafarauta daga kabilar Dogon sun hallaka akalla fulani 17, a wani hari da suka kai musu a kauyen Somena.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.