Isa ga babban shafi
Mali

Keita zai sake tsayawa takara a zaben Mali

Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana wa al’ummar kasar cewar zai tsaya takarar zaben da za ayi a watan Yuli mai zuwa.

Ibrahim Boubacar Keïta na Mali
Ibrahim Boubacar Keïta na Mali Ahmed OUOBA / AFP
Talla

An dade ana rade-radin cewar shugaban mai shekaru 73 zai tsaya takarar, amma ya ki cewa komai har sai a daren jiya da ya shaida wa al’ummar kasar ta kafar talabijin aniyarsa.

Mutane sama da 12 suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar, cikin su har da shugaban 'yan adawa Soumaila Cisse, wanda tsohon ministan kudi ne da Modibbo Kone, jami’in bankin Afrika ta Yamma.

Tun shekarar 2013 ake saran gudanar da zabe amma ake dagewa saboda matsalar tsaron da ta addabi kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.