Gwamnatin Mali ta tsaida ranar zaben shugaban kasa
Gwamnatin Mali ta bada tabbacin cewa zaben shugabancin kasar zai gudana a ranar 29 ga watan Yuli mai zuwa, idan kuma akwai bukatar gudanar da zaben zagaye na biyu, zai gudana ne ranar 12 ga watan Agusta.
Wallafawa ranar:
Sanawar ta zo ne bayan da majalisar kasar ta Mali, ta amince da shirin gwamnati da Fira Minista Soumelou Boubeye Maiga ya gabatar mata.
A jawadalin da gwamnati ta fitar, za’a soma yakin neman zabe daga ranar 7 zuwa 27 na watan Yulin.
Sau da dama gwamnatin Mali ta dage zaben shugabancin kasar tun daga shekarar 2013, saboda fuskantar matsalolin tsaro, a dalilin hare-haren kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a kasar, wadanda a cikin shekaru biyu da suka wuce, suka bazu daga arewaci zuwa tsakiya, da kuma kudancin kasar.
Kafin wannan lokacin dai, cikin shekarar 2012, kungiyoyin mayakan da ke da alaka da Al Qaeda suka kwace iko da yankin arewacin kasar Mali, kafin daga bisani rundunar soji, a karkashin jagorancin Faransa su kore su daga mafi akasarin yankunan da suka kwace.
A cikin watan Maris da ya gabata ne gwamnatin kasar ta Mali, ta dage zaben larduna da aka shirya gudanar da shi a Afrilu zuwa karshen wannan shekara ta 2018.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu