Nijar
'Yan Mali sama da dubu 8 sun tsallaka cikin Nijar
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla 'yan kasar Mali sama da dubu 8 suka tsallaka Tilaberi da ke Jamhuriyar Nijar domin kauce wa tashin hankalin da ake samu na hare haren 'yan ta’adda.
Wallafawa ranar:
Talla
Ofishin Jinkai na Majalisar yace, daga watan Janairu zuwa yanzu, mutanen da suka rasa matsugunansu sun kai dubu 8 da 432 sakamakon hare -haren da yan ta’adda ke kaiwa.
Majalisar tayi gargadin cewar adadin na iya tashi zuwa dubu 40 ganin yadda yankin ke dauke da wasu 'yan gudun hijira daga Mali tun bayan barkewar tashin hankali a shekarar 2012.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu