Isa ga babban shafi

Canada zata aike da dakarunta zuwa Mali

Canada ta ce nan gaba kadan, zata hada gwiwa da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali, inda zata aika da jiragen yaki, sojojinta da kuma jami’an lafiya zuwa kasar, don tallafawa yakin da ake da ta’addanci.

Jami'an sojin kasar Canada.
Jami'an sojin kasar Canada. Ints Kalnins/Reuters
Talla

A gobe Litinin ake sa rana Fira Ministan kasar ta Canada Justin Trudeau, zai sanar da daukar matakin a hukumance.

Tun a shekarar 2016, Trudeau ya yi alkawarin tura sojin kasar kimanin 600 zuwa Mali don aiki tare da dakarun Majalisar Dinkin Duniya wajen yakar ta’addanci.

Zuwa yanzu sama da dakarun wanzar da zaman lafiya 80, masu tada kayar baya suka hallaka, tun daga shekarar 2013, daya daga cikin abu amfi muni ga tarihin ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.