An fara kidayar kuri'un zaben shugabancin Mali
An fara aikin tattara sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na farko da aka gudanar ranar Lahadi, 29 ga watan Yuli na 2018, a kasar Mali.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan takara 23 ne suka fafata da shugaban kasar mai ci Ibrahim Boubacar Keita.
Bayanai na nuni da cewa zaben ya gudana cikin tsanaki a cikin manyan birane. Sai dai mahara sun harba makamai masu linzami kan garin Aguelhok da ke arewacin kasar.
A garin Lafia da ke yankin Timbuktu kuwa wasu gungun mutane ne sun kone kayayyakin zabe, sakamakon wata hatsaniya da ta tashi.
Tcheble Drame shi ne shugaban jam’iyyar adawa ta URD, kuma ya ce akwai daruruwan rumfuna da ba a gudanar da zabe a cikinsu ba.
Tcheble Drame shugaban jam’iyyar adawa ta URD a Mali
Souma’ila Cisse, tsohon ministan kudin Mali, shi ne babban abokin hamayyar shugaba Boubacar Keita a zaben na bana, wanda ya yi rashin nasara a zaben shugabancin kasar ta Mali da ya gudana a shekarar 2013 da gagarumin rinjaye.
Idan har aka kammala kidayar kuri’un da aka kada kuma babu dan takarar da ya lashe sama da kashi 50, za a sake gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu a ranar 12 ga watan Agusta mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu