Isa ga babban shafi
Mali

Larabawa sun yi zanga-zanga a Mali

Wasu matasa daga kabilar Larabawa sun gudanar da zanga-zanga a birnin Timbuktu da ke kasar Mali, in da suka yi ta harbin bindiga a sararin samaniya tare da  kona tayoyi da kuma motoci, kwanaki kalilan kafin gudanar da zaben shugaban kasa.

Matasa 'yan kabilar Larabawa sun kona motoci da tayoyi a yayin wata zanga-zanga kan tabarbarewar tsaro a Mali
Matasa 'yan kabilar Larabawa sun kona motoci da tayoyi a yayin wata zanga-zanga kan tabarbarewar tsaro a Mali HABIBOU KOUYATE / AFP
Talla

Wadannan matasa 'yan kabilar Larabawa wadanda akasarinsu 'yan kasuwa ne, na zanga-zangar ne saboda abin da suka kira tabarbarewar tsaro da kuma yadda jami’an tsaron ke cin zarafin fararen hula a yankin arewacin Mali da ke fama da tashin hankali.

Zanga-zangar ta tilasta wa mutane rufe shagunansu da bankuna, yayin da wasu suka koma gidajensu domin kauce wa harbe-harben da ake yi da bindiga.

Magajin Garin Timbuktu, Abacrine Cisse, wanda ya yi Allah wadai da zanga-zangar ya bayyana cewar, yana tintibar shugabannin kabilun yankin domin ganin sun shawo kan matasan da su kwantar da hankalinsu.

A karshen wannan mako ne ake gudanar da zaben shugaban kasa, in da shugaba Ibrahim Boubacar Keita zai fafata da 'yan takara da dama.

Shugaban ya ce, an fara samun zaman lafiya a yankunan kasar da ke fama da tashin hankali sakamakon girke rundunar G5 Sahel da kuma sojojin Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.