Isa ga babban shafi
Mali

An kaddamar da yakin neman zaben Shugaban kasa a Mali

A yau asabar ne aka kaddamar da yakin neman zaben Shugaban kasa a Mali,Zaben Shugaban kasar da yan takara 24 ne suka samu cika sharrudan da aka gindaya mu su,yan takaren za su yi kokarin shiga sako da lungunan kasar domin samun goyan baya da ya dace na lashe zaben.

Yan Mali na gudanar da rijista dangane da zaben kasar
Yan Mali na gudanar da rijista dangane da zaben kasar Michele CATTANI / AFP
Talla

Daya daga cikin matsallolin da ake sa ran yan takaran za su fuskanta shine na isa yankunan arewacin kasar da ma tsakiya ,yankunan dake fama da matsallar tsaro.

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa akala kashi 15 ne na mutanen kasar suka samu damar karbar katunan zabe, wanda hakan ke nuna rashin bayar da hadin kai daga yan kasar ta Mali.

Hukumar wanzar da zaman lafiya ta majalisar Dinkin Duniya a Mali Minusma ta soma bayar da horo zuwa masu sa ido a harakokin da suka shafi zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.