Isa ga babban shafi
Mali

Ankai hari kan ayarin sojoji masu rakiyar sakamakon zaben kasar Mali

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan ayarin jami’an tsaro da ke rakiyar kayayyakin zabe a yankin Segou da ke kasar Mali, inda rahotanni ke cewa an kashe sojoji 4 a yayin da wasu da motocinsu suka bata.

Sojojin Mali, a watan yulin  2018, Bamako.
Sojojin Mali, a watan yulin 2018, Bamako. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Lamarin dai ya faru ne a lokacin da jami’an hukumar zaben da ke tare da rakiyar sojoji ke dauke da kayayyakin sakamakon zabe ke hanyarsu ta zuwa birnin Bamako inda ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa da nan ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar lahadin da ta gabata a kasar.

Rahotanni sun ce baya ga sojoji 4 da suka rasa rayukansu, an kashe ‘yan bindiga akalla 8 a lokacin faruwar lamari, yayin da motocin soji 2 suka bata.

Wasu bayanai kuma na cewa, yanzu haka ana cigaba da neman wani adadin sojojin da ke cikin wannan ayari, da ake jin cewa sun bata ne a artabun da ya biyo bayan hari na kwanton bauna.

Wannan ne dai, shine hari na karo, da aka kai kan ayarin jami’an hukumar zaben a daidai lokacin da suke aikin tattara sakamakon zaben shugabancin kasa da nay an majalisar dokokin da aka gudanar a ranar lahadi 29 ga watan yulin 2018 a kasar ta Mali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.