Isa ga babban shafi
Ghana

An fara zaben Ghana

A yau ranar 1 ga watan Disamba ake fara gudanar da zaben shugaban kasar Ghana, inda jami’an tsaro da ‘yan Jaridu da za su yi aiki ranar zaben, za su fara kada kuri’unsu. Wannan ya sa hukumar zaben ta yi bayani kan tsarin zaben, kamar yadda wakilin RFI Ridwanullah Mukhtar Abbas ya aiko da rahoto daga Accra.

Ghana na amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a
Ghana na amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a Daniel Finnan
Talla

01:34

An fara zaben Ghana

Ridwanullah Abbas

Yayin da ya rage mako guda a gudanar da zaben shugaban kasar Ghana, babban dan adawar kasar Nana Akufo-Addo ya kauracewa mahawarar da aka shirya yi, abin da ya bai wa shugaban kasa John Dramani Mahama da wasu Yan takara 4 fafatawa a tsakanin su.

Masu sa ido a zaben na bayyana cewar za’a fafata tsakanin manyan yan takarar biyu saboda rashin gamsuwa da wasu ‘yan kasar ke da shi na tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

Shugaba Mahama ya tabbatar da matsalar wadda ya ce gwamnatinsa na iya bakin kokarinta wajen magancewa, yayin da Addo ke danganta matsalar da gazawar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.