Isa ga babban shafi
Syria

Taro kan tsara sabuwar hanyar magance rikicin Syria

A yau asabar aka soma wani zama dan sake tsara hanyar da za a bi don kawo karshen yakin Syria na sama da shekaru biyar a birnin Lausanne dake a kasar Switzerland.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov REUTERS/Darren Ornitz
Talla

Hakazalika sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai gana da takwaransa na Rasha Sergie Lavrov da wasu wakilan Majalisar Dinkin Duniya dama wasu shugabanin yankin.

Wannan dai na a matakin farfado da tattaunawar da ta ruguje a watan da ya gabata.

A can kasar Syria kuwa ana ci gaba da kai hare hare ba kakkautawa a birnin Aleppo.

Mutane fiye da dubu dari uku ne suka mutu a yakin Syria na sama da shekaru biyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.