Isa ga babban shafi
Syria-Rasha-Amurka

MDD na tattauna batun tsagaita wuta a Aleppo na Syria

Komitin Sulhu na MDD na shirin jefa kuri'a dangane da wasu kudirori biyu da suka shafi kasar Syria yau Asabar.

Babban Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon
Babban Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Kudiri na farko, kasar Faransa ce ta gabatar dake bukatar a gaggauta tsagaita wuta a Aleppo sannan sai kudiri daga kasar Rasha dake adawa gameda bukatar  kasar Faransa game da tsarin tsagaita wutan.

Ana ganin Rasha za ta yi amfani da karfin kujeran ta domin hana Daftarin kudirin da Faransa ta gabatar wanda Amurka da Britaniya ke goyon baya dake neman a hana dukkan zirga-zirgan jiragen sama na soji a Aleppo.

Jakadan Britania Matthew Rycroft yayi watsi da daftarin da Rasha ta gabatar a matsayin was an siyasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.