Isa ga babban shafi
MDD-Syria

MDD na nazarin daftarin Faransa kan yakin Syria

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na nazarin wani daftari da kasar Faransa ta gabatar kan yadda za a tilasata wani sabon shirin tsagaita wuta a Aleppo, sai dai Rasha ta yi watsi da shirin wanda ta bayyana shi a matsayin siyasa kawai.

Rayuka na cigaba da salwanta a Aleppo
Rayuka na cigaba da salwanta a Aleppo KARAM AL-MASRI / AFP
Talla

Shi dai wannan sabon yunkuri na kasar Faransa shine na baya bayan nan wajen ganin an tilastawa Rasha da kawarta Syria wajen ganin sun kawo karshen hare haren saman da suke kai wa Aleppo, wanda ya gamu da suka daga kasashen duniya.

Ana saran daftarin ya goyi bayan shirin hadin kai tsakanin Amurka da Rasha na kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 5 anayi, wanda ya hallaka mutane 300,000 ya kuma raba mutane miliyan 12 da gidajen su.

Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Gennady Gatilov ya ce su basa goyan bayan yunkurin na Faransa wanda babu komai cikin sa sai siyasa.

Ita ma kasar Amurka ta ce hakurin ta ya kare kan hadin kan da Rasha saboda yadda ta ke ci agba da kai hare hare kan fararen hula.

Rasha na zargin Amurka da goyan bayan ISIS, yayin da Amurka ke zargin Rasha da taimakawa shugaba Assad ci gaba da zama a kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.