Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Rasha ta gargadi Amurka kan yunkurin kawar da gwamnatin Assad

Rasha ta ja hankalin Amurka kan daukar matakin  tunbuke gwamnatin shugaba Bashar Al-assad ganin irin illar da zai yi  bama ga kasar Syria kadai ba har da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya.

Shekaru fiye da biyar da barkewar yaki a Syria, mutane sama da 300,000 sun mutu
Shekaru fiye da biyar da barkewar yaki a Syria, mutane sama da 300,000 sun mutu AMEER ALHALBI / AFP
Talla

Mai Magana da yawun ministan ma’aikatar harkokin cikin gidan Rasha Maria Zakharova ce ta sanar da hakan inda ta fayyace illolin kawar da gwamnatin Assad ta hanyar anfani da karfi da Amurka ke yunkurin yi.

Zakharova ta kara da cewa da zarar Amurka ta yi nasarar kawar da Assad daga mulki ‘yan ta’adda ne zasu karbe iko su kuma ci karensu babu babbaka.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake cigaba da tafka fada a tsakanin dakarun gwamnati dake samun goyon bayan sojin Rasha da ‘yan tawaye a birnin Aleppo.

Rahotanni na cewa an samu fashewar bama bamai a wani babban asibiti dake tsakiyar birnin Aleppo sakamakon hare hare ta sama da ake ta kaiwa da jiragen yaki.
Shekaru fiye da biyar da barkewar yaki a Syria, mutane fiye da dubu dari uku ne suka mutu baya ga miliyoyi da suka rasa matsuguni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.