Isa ga babban shafi
Rasha-Syria

Rasha zata tura karin jiragen yaki zuwa Syria

Yayinda Rasha ke fuskantar suka daga Amurka kan rawar da take takawa a yakin Syria, rahotanni sun ce Rashan zata tura karin jiragen yaki zuwa Syrian, a kokarinta na murkushe mayakan ‘yan tawayen kasar.

KARAM AL-MASRI / AFP
Talla

Yanzu haka ana cigaba da gwabza fada tsakanin sojin Syria da Rasha ke goya baya da ‘yan tawayen kasar murkushe tunga ta karshe ta ‘yan tawayen a gabashin birnin Aleppo.

A gefe guda kuma Ministan harkokin waje na Rasha Sergei Lavrov ya zargi Amurka da goyon bayan ‘yan tawayen Syria domin kawar da Shugaba Basshar Assad daga mulki.

Rahotanni sun ce akalla karin fararen hula 23 sun rasa rayukansu a cigaba da fadan da ake gwabzawa a Aleppo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.