Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen duniya sun soki Rasha kan rikicin Syria

Kasashen Faransa da Birtaniya da Amurka sun caccaki Rasha kan tabrbarewar al’amura a Syria sakamakon hare-hare mafi muni da jiragenta suka kai, abinda ya hallaka mutane da dama.

Rikicin Syria ya hallaka mutane fiye da dubu 300 a cikin shekaru biyar da suka wuce
Rikicin Syria ya hallaka mutane fiye da dubu 300 a cikin shekaru biyar da suka wuce REUTERS/Sultan Kitaz
Talla

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta zargi Rasha da rashin imani a lokacin da aka gudanar da taron kwamitin sulhu na gaggawa don ganin Rashar ta ja kunnen shugaban Syria Bashar al Assad da kuma daina kai hare-hare.

Power ta ce, a maimakon neman hanyar zaman lafiya, Rasha da abokin tafiyarta Bashar al Assad, sun mayar da hankali don ci gaba da yaki, in da ta ce, matakan da Rasha ke dauka ba yaki da ta’addanci ba ne, sai dai aika-aika.

Shi kuwa Jakadan Faransa Francois Delattre, zargin aikata laifufukan yaki ya yi, in da ya bukaci hukunta wadanda ake zargi.

Jakadan Birtaniya Matthew Rycroft cewa ya yi, yana da wahala ace Rasha ba ta hada kai da Assad wajen aikata laifufukan yaki ba.

A na shi martanin, jakadan Rasha Vitaly Churkin ya zargi Amurka ne da kasa fada wa 'yan tawayen da ke dauke da makamai da su nesanta kansu da kungiyar al-Nusra da kuma daina kai hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.