Isa ga babban shafi
Najeriya - Wasanni

Wasan Najeriya da Ghana : Wani jami'in FIFA ya mutu a filin wasan Abuja

Wani jami’in hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma Hukumar CAF ta Africa, Dr Joseph Kabungo ya mutu ranar Talata a Abuja sakamakaon bugun zuciya bayan kammala karawa tsakanin Najeriya da Ghana a gasar neman zuwa cin kofin duniya.

Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar Najeriya super eagle yayin wasan da aka fafata tsakanin Ghana da Najeriya a Abuja
Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar Najeriya super eagle yayin wasan da aka fafata tsakanin Ghana da Najeriya a Abuja © NFF
Talla

Dr Kabungo wanda ‘dan assalin kasar Zambia ne na jagorancin kwamitin dake sa ido akan ‘yan wasan dake amfani da miyagun kwayoyi ne dangane abinda ya shafi karawar ta ranar Talata.

Tuni Hukumar kwallon kafar Najeriya ta aike da sakon ta’aziya ga Hukumar FIFA da CAF dangane da mutuwar jami’an, inda ta bayyana kaduwar ta da lamarin.

Wasan Najeriya da Ghana

Sanarwar da mai magana da yawun Hukumar NFF a Najeriya Ademola olajiri ya gabatar, tace jami’in dake kula da bangaren kula da lafiyar Hukumar, Dr. Onimisi Ozi Salami ya shaida mata cewar an sami Dr Kabungo ne yana numfashi sama sama kusa da dakin da ‘Yan wasan Ghana ke shiryawa a filin wasan Abuja, abinda ya sa aka bada umurnin gaggauta kai shi asibiti, amma kuma kafin a isa, rai yayi halin sa.

Sanarwar ta bayyana Dr. Ozi Salami na cewar, lamarin ya faru ne a daidai lokacin da yake neman ‘dan wasan Najeriya domin daukar samfurin sa, yayin da shi Dr Kabungo ke neman ‘dan wasan Ghana.

Matsalar numfashi

Sanarwar tace Babban jami’in kula da wasan Kabore Hubert Bosilong daga Afirka ta Kudu ya janyo hankalin Dr. Salami lokacin da ya fahimci cewar likitan ya fara fuskantar matsalar numfashi, kuma Babban jami’in tsaron FIFA dake kula da wasan Mr Dixon Adol Okello ya shaida abinda ya faru.

Olajire yace bayan kokarin farfado da Dr. Kabungo ya gagara, sai suka dauke shi a cikin motar kula da marasa lafiya domin kai shi asibitin Cedar Crest dake Apo inda yace ‘ga garun ku nan’.

Ba 'yan kallo bane suka kashe shi

Hukumar kwallon kafar Najeriya tayi watsi da zargin cewar 'Yan kallo ne suka lakada masa duka, abinda yayi sanadiyar mutuwar sa, inda tace ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

Hukumar tace jami’an ta da na ofishin Jakadancin Zambia sun gudanar da taro yau da safe domin sanin matakin da zasu dauka nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.