Isa ga babban shafi

Hukumar shirya Olympic OIC ta dakatar da Ahmad Al Sabah tsawon shekara 15

Hukumar shirya wasannin motsa jiki na Bazara Olympic wato OIC, ta dakatar da shugaban hukumar kasar Kuwait Sheikh Ahmad Al- Sabah na tsawon shekaru 15.

Tsohon jami'in hukumar kwallon kafa ta Duniya, Al-Sabah
Tsohon jami'in hukumar kwallon kafa ta Duniya, Al-Sabah © AFP or Licensors
Talla

An dau Matakin dakatar da Al-Sabah, daga shiga aiyyukan da suka shafi hukumar tsawon shekarun ne, sakamakon samun sa da laifin karya dokoki da ka'idojin hukumar ta OIC.

Tsohon jami'in hukumar kwallon kafa ta Duniya, Al-Sabah, yanzu haka Yana fuskantar tuhume tuhume Daban -daban, a Kotun kasar Switzerland.

Ahmad Al-Sabah
Ahmad Al-Sabah REUTERS - Arnd Wiegmann

Ta cikin wata Takarda da aka aikewa dukkanin jami'an hukumar ta OIC, Wacce Kamfanin Dillacin Labarai na Rueters ya samu kwafin ta, jami'in gudanarwa na hukumar Christophe De Kepper, ya tabbatar da dakatarwar.

Ko a shekarar bara ta 2023, an dakatar da Al-Sabah, na tsawon shekaru 3, sakamakon rawar da ya taka wajen juya akalar Zaben hukumar ta Olympic na kasashen Nahiyar Asiya, musamman ma wajen Karan Tsaye ga ka'idojin hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.