Isa ga babban shafi
Kwallon Ƙafa

Real Madrid ta lashe kofin La Ligar Spain karo na 36

Real Madrid ta lashe kofin gasar ƙwallon ƙafar La Ligar Spain bayan da ta samu nasara a  kan Cadiz da ci 3 da nema, kana Girona ta lallasa Barcelona da ci 4 da 2 a ranar Asabar, nasarar da kocin Madrid ɗin, Carlo Ancelotti ya bayyana a matsayin cancanta.

Wasu ƴan wasan Real Madrid, Joselu da Nacho Fernández su na murnar lashe kofin La Ligar Spain karo na 36.
Wasu ƴan wasan Real Madrid, Joselu da Nacho Fernández su na murnar lashe kofin La Ligar Spain karo na 36. © AFP / OSCAR DEL POZO
Talla

Tawagar ta Ancelotti ta yi aiki tuƙuru ta wajen doke Cadiz, kuma bayan da Girona ta bai wa abokiyar hamayyarta,, Barcelona mamaki da ci 4 da 2, aka miƙa mata wannan kofi, wanda karo na 36 kena take lashe shi tarihinta.

Wannan  nasarar mai mahimmanci da Girona ta samu ya sa yanzu ta samu gurbin fafatawa a gasar zakarun nahiyar Turai a a karo na farko a tarihinta, a cikin kaka ta 4 kawai da ta fafata a gasar La Ligar Spain.

Ancelotti ya hutar da ƴan wasa masu mahimmmanci a wannan wasa da ya fafata sakamakon yadda ya ke sa ran karawa da Bayern Munich a zubi na 2 na wasan kusa da ƙarshe a gasar zakarun nahiyar Turai a wannan mako, amma kuma ƴan wasa da ya saka suka bada abin da ake buƙata.

Brahim Diaz e ya fara ci wa Madrid ƙwallo a minti na 51 da fara wasa, kana ya taimaka wa Jude Bellingham ya ci ta biyu, Joselu kuma ya ci ta uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.