Isa ga babban shafi

Wasan PSG da Dortmund a yau ka iya zama na karshe da Mbappe zai dokawa kungiyar

A yau Talata ne ake sa ran kungiyar Kwallon kafa ta PSG za ta karbi bakucin Borussia Dortmund a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Kylian Mbappé célèbre l'égalisation parisienne contre le FC Barcelone avec Ousmane Démbélé en quart de finale aller de la Ligue des champions, le 10 avril 2024.
Kylian Mbappé célèbre l'égalisation parisienne contre le FC Barcelone avec Ousmane Démbélé en quart de finale aller de la Ligue des champions, le 10 avril 2024. REUTERS - Stephanie Lecocq
Talla

Tun da farko kungiyar ta Faransa ta sha kashi a hannun tawagar ta Jamus da ci 1 da nema, a haduwar farko da suka yi ranar 1 ga watan nan da muke ciki.

Sai dai masu sharhi na kallon akwai yiwuwar PSG ta iya sauya sakamakon wasanta a yau din.

Haduwar ta yau dai ka iya zama wasan karshe da Kylian Mbappe zai dokawa PSG karkashin gasar zakarun Turai, dai dai lokacin da ya ke gab da kawo karshen zamaninsa a kungiyar.

Idan har PSG ta iya sauya sakamakon har ta kai ga wasan karshe na gasar, da za ta hadu da ko dai Real Madrid ko kuma da Bayern Munich kenan zakaran na Faransa zai iya samun damar lashe kofin karon farko a tarihi.

Yan wasan PSG
Yan wasan PSG © AFP / FRANCK FIFE

Kazalika karo na biyu da wata kungiya daga Faransa za ta lashe kofin tun bayan da Marseille ta lashe a shekarar 1993.

Bugu da kari akwai yiwuwar tarihi ya maimaita kansa idan har kungiyoyin PSG da Bayern Munich suka tsallaka wasan karshe, wato irin haduwarsu ta shekarar 2020 a Lisbon lokacin da tawagar ta Jamus ta doke tawagar ta Faransa da kwallo 1 da nema tare da lashe kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.