Isa ga babban shafi

PSG na fatan sauya sakamakon wasanta da Borussia Dortmund a Parc des Princes

Masu sharhi na ci gaba da mabanbantan tsokaci kan yiwuwar PSG ta iya sauya sakamakon wasanta da Borussia Dortmund a haduwarsu ta gobe Talata karkashin gasar cin kofin zakarun Turai lokacin da kungiyar ta Jamus za ta yi tattaki zuwa filin wasa na Parc des Princes bayan tun farko ta doke tawagar Faransa a haduwar farko da kwallo 1 mai ban haushi.

'Yan wasan PSG.
'Yan wasan PSG. © AFP / FRANCK FIFE
Talla

Haduwar ta gobe dai wala’alla ta zama wasan karshe da Kylian Mbappe zai dokawa PSG karkashin gasar zakarun Turai dai dai lokacin da ya ke gab da kawo karshen zamaninsa a kungiyar ko kuma ya zama tubalin da kungiyar za ta dogara da shi wajen kai wa wasan karshe na gasar da zai gudana a filin wasa na Wembley da ke Jamus.

Idan har PSG ta iya sauya sakamakon har ta kai ga wasan karshe na gasar, da za ta hadu da kodai Real Madrid ko kuma Bayern Munich kenan zakaran na Faransa Kylian Mbappe zai iya samun damar iya lashe kofin karon farko a tarihi, haka zalika karo na biyu da wata kungiya daga Faransa za ta lashe tun bayan Marseille a shekarar 1993.

Bugu da kari akwai yiwuwar tarihi ya maimaita kansa idan har kungiyoyin PSG da Bayern suka tsallaka wato kwatankwacin haduwarsu ta shekarar 2020 a Lisbon lokacin da tawagar ta Jamus ta doke tawagar ta Faransa da kwallo 1 mai ban haushi tare da lashe kofin.

Gaban ‘yan kallo dubu 90 ne za a doka wasan karshe tsakanin kungiyoyi 2 da suka iya tsallake wannan mataki na wasan gab da na karshe, daga cikin kungiyoyin 4 da yanzu haka suka rage kuma kafar PSG guda ke waje sabanin Madrid da Munich wadanda suka yi canjaras ita kuma Munich ke da nasara a haduwar farko.

Bayan matakinsa na sanar da raba gari da PSG a karshen wannan kaka, fata daya da tauraron na Faransa ke da shi shi ne ganin ya lashewa kungiyar kofin zakarun turai wanda ya gaza lashewa a tsawon kakar wasa 7 da ya shafe ya na takawa kungiyar leda bayan sayo shi daga Monaco a shekarar 2017, duk da kasancewarsa mafi zurawa kungiyar kwallo a tarihi da jumullar kwallo 255 a wasanni 305.

Sai dai wani babban kalubale ga Mbappe mai shekaru 25 shi ne yadda PSG ke fama da rashin sa'a musamman a irin wannan mataki lura da yadda aka yi waje da ita a irin wannan mataki sau 8 daga 2011 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.