Isa ga babban shafi

Real Madrid ta kai wasan karshe bayan doke Bayern Munich a gasar zakarun Turai

Ta tabbata kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta haska a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai karo na 18 a tarihi, bayan da tawagar ta Carlo Ancelotti ta doke Bayern Munich ta Jamus da kwallaye 2 da 1 a daren jiya, da jumullar kwallaye 4 da 3 a haduwa 2 da kungiyoyin 2 suka yi.

Joselu bayan zura kwallon da ta cirewa Real Madrid kitse a wuta.
Joselu bayan zura kwallon da ta cirewa Real Madrid kitse a wuta. AFP - THOMAS COEX
Talla

Yayin wasan na jiya har zuwa tafiya hutun rabin lokaci babu kungiyar da ta zura kwallo tsakanin manyan tawagogin biyu na Spain da Jamus, sai a minti na 68 Davies da taimakon Kane ya zura kwallo guda, amma kuma mintuna 10 tsakanin Joselu ya farke kwallon bayan sako sako shi a fili a matsayin musaya.

Kai tsaye za a iya cewa Joselu ne ya kai Real Madrid ga wasan na karshe lura da cewa shi ya sake zura kwallon ta biyu a karin lokaci da taimakon Rudiger, wanda kafin nan har an fara tsammanin Real Madrid ta sha kaye a Santiago Bernabeu tare da gaza samun damar kai wa wasan karshe na gasar.

Kai tsaye yanzu Real Madrid za ta kara da Borussia Dortmund ne a wasan karshe na gasar da zai gudana a filin wasan na Wembley a birnin London gaban ‘yan kallo dubu 90.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.