Isa ga babban shafi

Kuskuren Tuchel ne ya sanya Bayern Munich shan kaye - Ferdinand

Masu sharhi sun dora alhakin rashin nasarar Bayern Munich kan mai horarwa Thomas Tuchel, lura da yadda wasa ya rikice masa kasa da minti 3 bayan matakinsa na cire Harry Kane na Ingila daga fili, lokacin da suke jagoranci kuma suke rike da wasan da kwallo 1 da nema.

'Yan wasan Bayern Munich.
'Yan wasan Bayern Munich. AFP - KIRILL KUDRYAVTSEV
Talla

A cewar Rio Ferdinand abin tausayi ne yadda fatan Kyaftin din na Ingila ya gaza cika na ganin ya jagoranci tawagar ta shi zuwa mahaifarshi a wasan karshe na gasar da zai gudana a filin wasa na Wembley da ke birnin London.

Ferdinand tsohon dan wasan Ingila da ya taba lashe kofin zakarun Turai, ya ce wasan ya na tafiya dai dai ta bangaren Bayern Munich a wani yanayi da Real Madrid ta fara karaya amma kwatsam Tuchel ya yi sauyin da ya basu kwarin gwiwa.

Ferdinand ya ce bayan ficewar Kane da kuma sako Joselu da Ancelotti ya yi, Madrid ta samu kwarin gwiwa yayinda kuskuren Manuel Neuer ya bai wa tawagar ta birnin Madrid damar zura kwallo ta hannun Joselu lamarin da ya sake karfafa gwiwarsu tare da tsananta farmakin da suke kai wa kuma kasa da mintuna 3 suka sauya wasan.

Kai tsaye Harry Kane zai sake kammala kakar wasa ta bana ba tare da kofi ba, kwatankwacin halin da ya shiga a tsohuwar kungiyarsa Tottenham.

Ferdinand ya ce Kane ya yi duk abin da zai iya a wannan kaka domin kuwa ya ci kwallaye ya kuma taimaka anci wasu, kuma fata na karshe da ya rage masa shi ne ganin ya kai wasan karshe na gasar ta cin kofin zakarun Turai amma kuma mafarkinsa ya gaza zama gaskiya saboda kuskuren Tuchel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.