Isa ga babban shafi
Najeriya - Wasanni

Za'a gaggauta rufe ofisoshin gwamnati a Abuja don wasan Najeriya da Ghana

Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe ofisoshin gwamnati da ke Abuja daga karfe 1 na ranar wannan Talata,  domin nuna goyon baya ga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Super Eagles za ta kara da Black Stars ta Ghana.

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya AFP - DANIEL BELOUMOU OLOMO
Talla

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya fitar, dake cewa tawagar ta Najeriya na bukatan magoya baya yayin fafata wasan mai mutukar muhimmaci da zai kare martabar kasar.

Najeriya da Ghana zasu fafata a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a yammacin wannan Talata,  a wasan da ake saran yayi zafi tsakanin kasashen biyu dake hamayya na shekaru 71 da fafatawa 58, bayan haduwarsu ta ranar Jumma a Kumasin Ghana aka karkare mintuna 90 babu wanda ya ci wani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.