Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

'Yan wasan Super Eagles sun fara hallara don tunkarar wasansu da Ghana

Zuwa yanzu ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya akalla 18 ne suka hallara a sansanin atisayen kasar da ke birnin Abuja cikin ‘yan wasa 25 da kasar ta kira don tunkarar karawarsu da Black Stars ta Ghana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya
Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya © AP - Sunday Alamba
Talla

Wasan wanda zagayen farkonsa zai gudana ranar juma’a yayinda kwanaki 4 tsakani za a doka karawa ta biyu tsakanin bangarorin biyu da ke kokarin samun tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya karo na 22 da ke shirin gudana a Qatar.

Kaftin din tawagar Ahmed Musa da mataimakinsa Williams Ekong na jerin ‘yan wasan farko da suka hallara a Abuja, baya ga Leon Balogun da Oluwasemilogo Ajayi da kuma Olaoluwa Aina da Frank Onyeka.

Sauran ‘yan wasan da suka hallara sun hada da Odion Ighalo da Daniel Akpeyi da kuma Oghenekaro Etebo sai Kelechi Iheanacho da Abdullahi Shehu da kuma Francis Uzoho sai Moses Simon.

Sauran sun hada da Emmanuel Dennis da Joseph Ayodele-Aribo da kuma Calvin Bassey da Innocent Bonke da Kenneth Omeruo.

Za dai a doka wasan ne ba tare da mai tsaron ragar Najeriya lamba daya ba wato Maduke Okoye wanda aka maye gurbinsa da John Noble mai tsaron ragar Enyimba.

Najeriyar wadda ta dage kofin Afrika sau 3 za ta hadu da Ghanar wadda ta dage kofin sau 4 a filin wasa na Baba Yara mai daukar ‘yan kallo dubu 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.