Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Za mu dauko kofin Afrika daga Kamaru - Super Eagles

Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lashi takobin lashe kofin gasar kasashen Afrika da za a fara gudanarwa daga ranar 9 ga wannan wata na Janairu a Kamaru zuwa 6 ga watan gobe na Fabairu.

Najeriya ta lashe kofin AFCON har au uku a tarihi
Najeriya ta lashe kofin AFCON har au uku a tarihi REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Wani lokaci a yau ne tawagar ta Najeriya za ta kama hanyar zuwa can Kamaru domin halartar babbar gasar ta nahiyar Afrika.

Najeriya za ta yi wasanta na farko ne da Masar a rukunisu na D a ranar 11 ga watan nan, wasan da babu shakka zai dauki hankali matuka saboda zubin 'yan wasan da kowanne bangare ke tunkaho da su.

Mohamed Salah na Liverpool ne zai jagoranci tawagar Masar wadda ta lashe kofin gasar Afrika har sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku, amma take fatan sake lashewa a karo na hudu.

Kodayake masana harkokin wasan sun fara hasashen yadda za ta kaya a fafatawar tsakanin kasashen biyu, inda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ke cewa, da yiwuwar Najeriya ta samu nasara kan Masar da ci 2-1.

Alkaluma sun nuna cewa, sau biyu kacal Masar ta doke Najeriya a daukacin wasannin da kasashen biyu suka yi a gasar ta cin kofin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.