Kamaru: Mutane 8 sun mutu 50 sun jikkata dalilin turmutsitsi a filin wasa
Mutane 8 sun mutu yayin da wasu 50 suka jikkata a Kamaru, sakamakon turmutsitsi mutanen da ya auku a wajen filin wasan kwallon kafa na kasar da ke birnin Yaounde.
Wallafawa ranar:
Lamarin ya auku ne, a lokacin da cincinrindon jama’a suka yi yunkurin shiga filin ta wasan na Olembe da ke babban birnin kasar domin kallon wasan da Kamaru za ta kara da Comoros, wanda daga karshe mai masaukin bakin ta samu nasara 2-1.
Ma’aikatar lafiyar Kamaru ta ce, cikin mutanen 8 da suka mutu a turereniyar akwai mata biyu ‘yan shekara talatin, maza hudu suma da shekarunsu suka kai tallatin talatin, sai yaro daya, da kuma wani mutum da iyalansa suka tafi da gawarsa.
Ma'aikatar ta kara da cewa, cikin mutane 50 da suka jikkata, akwai wani jariri da aka tattake yayin turmutsitsi, sai dai an yi nasarar ceto ransa jaririn, tare da garzayawa da shi babban asibitin birnin Yaounde.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu