An gano dalilin da ya sa Alkali tsayar da wasan Tunisia da Mali sau biyu
Bayan shafe kwanaki ana cece-kuce akan Janny Sikazwe, alkalin wasa dan kasar da ya jagoranci wasan da aka buga tsakanin Tunisia da Mali a ranar Laraba, an gano dalilinsa na busa usur din kawo karshen fafatawar kafin lokaci ya cika har sau biyu.
Wallafawa ranar:
A ranar ta Laraba dai, Sikazwe ya fara kawo karshen wasan Tunusia da Mali ne a minti na 85, da kuma minti na 89, abinda ya janyo hayaniya daga bangaren tawagar kwallon kafar Tunisia.
Sai dai a yayin da yake karin bayani akan lamarin, shugaban alkalan wasan da ke alkalanci a wasannin gasar cin kofin Afirka, Essam Abdel-Fatah, ya ce alkali Janny Sikazwe yayi fama ne da matsalar tsananin zafin da makinsa ya kai 34 a ma’aunin Celcius abinda ya haifar da karancin ruwa a jikinsa.
Abdel-Fatah ya kara da cewar ko bayan Karkare wasan da Mali ta doke Tunisia da 1-0 a filin was ana Limbe da ke Kamaru, sai da aka gaggauta garzawaya da Alkali Sikazwe asibiti domin ceto lafiyarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu