Isa ga babban shafi
Wasanni - Kamaru

CAF ta gabatar da karin sabbin dokoki a gasar cin kofin Afirka

Kwamitin zartarwas hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ya sanar da sabbin ka'idoji kan yawan 'yan wasa da kuma wadanda za su maye gurbinsu yayin fafata wasanni a gasar AFCON.

Yadda aka yi bikin bude gasar cin kofin kasashen Afirka a birnin Yaounde na kasar Kamaru.
Yadda aka yi bikin bude gasar cin kofin kasashen Afirka a birnin Yaounde na kasar Kamaru. © AFP - KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, hukumar CAF ta ce dole ne kungiyoyin da ke cikin gasar cin kofin Afirka ta bana su buga wasanninsu idan suna da akalla 'yan wasa goma sha daya da basu kamu da Korona ba, la’akari da yadda aka rika samun ‘yan wasan da suka kamu da cutar yayin da ake gaf da fara wasannin gasar ta AFCON.

CAF ta kara da cewar, idan kuma babu mai tsaron raga a tawagar kwallon kafar kasa, za a bukaci dan wasan ciki ya koma raga ne, yayin da kuma a bangaren canjin ‘yan wasa hukumar kwallon kafar ta Afirka ta baiwa kasashe damar sauya adadin ‘yan wasa har 5 da karin 1 idan aka shiga zangon karin lokaci, yayin fafatawa a wasannin AFCON.

Daga cikin tawagogin kwallon kafar kasashen da suka ba da rahoton bullar cutar Korona a sansaninsu gabanin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka akwai, Kamarun mai masaukin baki, Algeria, Burkina Faso, Ivory Coast.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.