Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta rage adadin 'yan kallo a filayen wasanni yayin gasar AFCON

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF, ta gabatar da wasu sauye-sauye kan adadin ‘yan kallon da za su shiga filayen wasanni, da kuma batun karbar allurar rigakafin Korona, yayin gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika ta AFCON, da ake shirin farawa nan da dan lokaci a Kamaru.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe. Daniel Beloumou Olomo AFP
Talla

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Intanet, hukumar CAF ta ce za a kayyade yawan masu shiga filayen wasanni yayin gasar ta AFCON daga kashi 100 zuwa kashi 80 a wasannin da mai masaukin baki Kamaru za ta buga.

Kashi 60 cikin 100 na ‘yan kallo ne kuma za su baiwa idanunsu abinci kai tsaye a filaye yayin fafata wasannin sauran kasashe Afirka da ke halartar gasar ta AFCON, sai kuma tilasta nuna katin shaidar yin allurar rigakafin Korona da kuma gwajin ba sa dauke da cutar ga dukkanin masu halartar kallon wasannin gasar.

CAF ta ce matakin ya biyo bayan ganawa da gwamnatin Kamaru da kuma sauran masu ruwa da tsaki dangane da dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Gabanin bude wasa tsakanin Kamaru da Burkina Faso a ranar 9 ga watan Janairu a filin wasa na Olembe na birnin Yaounde dai, tawagogin kwallon kafar kasashe da dama ne suka ba da rahoton kamuwar wasu daga cikin ‘yan wasansu da cutar Korona, cikinsu har da Kamarun mai masaukin baki, Algeria da kuma Cape Verde.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.