'Yan bindiga sun yi wa 'yan jarida uku fashi a Kamaru yayin gasar AFCON
‘Yan bindiga da sun yi wa wasu ‘yan jarida uku daga kasar Algeria fashi, tare da yin amfani da wuka wajen jikkata su a daren ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran kasar Algeria na APS ya ruwaito cewar, ‘yan jaridar da ke aikin daukar labaran gasar cin kofin kasashen Afrika a Kamaru, sun gamu da tashin hankalin ne, a yayin da suke barin dakunan otal dinsu da ke birnin Douala.
Baya ga jikkata ‘yan jaridar da suka yi, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da jakar kudaden ‘yan Algerian, da wayoyi da kuma Komfutocinsu.
A halin da ake ciki hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta ta hada gwiwa da jami’an tsaro wajen gudanar da binicke akan lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu