TikTok ya shiga jerin masu daukar nauyin gasar AFCON
Kamfanin TikTok ya sanar da kulla yarjejeniyar kasuwanci ta tsawon shekara guda da hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF.
Wallafawa ranar:
Matakin ya sanya kamfanin shiga jerin masu daukar nauyin gasar cin kofin kasashen Afirka da ake shirin farawa a kasar Kamaru.
A karkashin wannan yarjejeniya dai, TikTok, sabon dandalin da yayi fice wajen wallafa takaitattun hotunan bidiyo zai kasance cikin masu daukar nauyi da kuma tallata kansa a gasar cin kofin Zakarun kungiyoin kasashen Afirka a shekarar bana, da kuma gasar cin kofin kasashen Afirka ajin mata da kasar Morocco za ta karbi bakunci a tsakanin 2 zuwa 23 ga watan Yulin shekarar 2022 da muke ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu