Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

FIFA na tattaunawa da CAF kan makomar gasar kofin kasashen Afirka

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino, ya bayyana cewa tawagarsa na tattaunawa da hukumar kwallon kafar Afirka CAF da kuma sauran masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar cin kofin kasashen nahiyar na shekarar 2021, domin ganin ko za a iya dage gasar zuwa watan Satumba.

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino. Harold Cunningham FIFA/AFP
Talla

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da shakku ke kara yin karfi dangane da yiwuwar gudanar gasar ta AFCON kamar yadda aka tsara a Kamaru, a yayin da ya rage kasa da makwanni uku kafin a soma wasannin a cikin watan Janairun da ke tafe.

Bangaren da ya fi nuna adawa da gudanar gasar cin kofin Afirkan dai shi ne Turai, inda kungiyoyin nahiyar suka yi tsayuwar gwamen Jaki musamman na Ingila, kan aniyarsu ta kin sakin manyan ‘yan wasan da ke taka musu leda domin wakilatar kasashensu.

Zalika batun yaduwar sabon nau’in cutar Korona na Omicron na daga cikin dalilan da ya sa wasu ke neman a dage lokacin gudanar gasar cin kofin ta kasashen Afirka.

Tuni dai a baya aka dage gasar ta AFCON har sau biyu saboda annobar ta Korona

A jiya Litinin kuma shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, ya bayyana cewar gudanar gasar AFCON a cikin watan Janairu ya zama matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.