Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Kamaru ta musanta shirin janyewa daga karbar bakuncin gasar AFCON

Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana ganawa da hukumar kwallon kafar Afirka CAF dangane da yiwuwar janyewa daga karbar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afirka ta AFCON, saboda barkewar sabon nau’in cutar Korona na Omicron a sassan kasar.

Samuel Eto'o sabon shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Kamaru.
Samuel Eto'o sabon shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Kamaru. Daniel Beloumou Olomo AFP
Talla

Yayin wata hira a ranar Alhamis, da kafar watsa labaran wasanni ta FilGoal da ke kasar Masar, kakakin ma’aikatar wasanni ta Kamaru Buthi Minsip, ya ce tuni ministan wasanni ya gana da Samuel Eto'o, shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru, domin tabbatar da shirye-shiryen Kamaru na karbar bakuncin gasar tare da yin watsi da dukkan zarge-zargen da ake yi na yiwuwar rashin gudanar da gasar AFCON a karkashin karbar bakuncin Kamaru.

Dangane da barazanar da kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai ke yi kuwa na hana ‘yan wasa zuwa wakilcin kasashensu a gasar ta cin kofin Afirka saboda yaduwar cutar Korona, Minsip ya bayyana matakin a matsayin mugunta tsaba, ta hanyar kafa hujja da bayanai marasa tushe ballantana makama.

A halin da ake ciki, tsanantar sabon nau’in cutar Korona na Omicron ya janyo samun karuwar kungiyoyin Firimiya da ke neman a dage musu wasanninsu zuwa cikin sabuwar shekara ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.