Isa ga babban shafi
Afrika-AFCON

CAF na shirin fitar da jadawalin gasar cin kofin Afrika na 2022

Yau Talata hukumar kwallon kafar Afrika ke shirin fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar wanda Kamaru za ta karbi bakonci a wannan karon, gasar da ke kunshe da kasashe 24 wadanda za a rabasu zuwa rukunnai 4 kowanne dauke da kasashe 6-6.

Kofin gasar Zakarun kungiyoyin nahiyar Afirka.
Kofin gasar Zakarun kungiyoyin nahiyar Afirka. © REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Kamar yadda ya ke bisa tsari kasashen 24 za su shiga rukunnansu ne bisa la’akari da matsayinsu a matakin kwarewa da FIFA ke fitarwa.

Bayanai na nuna cewa taron fitar da jadawalin gasar da zai gudana a Kamaru zai samu halartar manyan-manyan ‘yan wasan nahiyar ta Afrika ciki har da Samuel Eto da Didier Drogba da Yaya Toure da kuma Jay Jay Okocha.

Za dai a faro gasar daga ranar 9 ga watan Janairun 2022 zuwa 6 ga watan Fabarairu.

Hasashe dai na nuna da yiwuwar Senegal da ke matsayin jagorar kwallon kafa a matsayin da FIFA kan fitar ta shiga rukunin farko tare da mai masaukin baki Kamaru kana Algeria mai rike da kambu da kuma Tunisia baya ga Najeriya da Marocco.

Rukuni na biyu da yiwuwar ya kunshi kasashen Masar Ghana Cote d’Ivoire da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea

Rukuni na 3 zai iya kunsar Cape Verde da Gabon da Mauritania da Sierra Leone da zimbabwe da Guinea bissau.

Sai rukuni na 4 da zai iya kunsar Malawi da Sudan da Equatorial Guinea da Habasha da Gambia da kuma tsibirin Comoros.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.