Isa ga babban shafi
Wasanni - CAF

CAF ta dakatar da Chadi daga wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Afrika

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF, ta haramta wa Chadi ci gaba da sauran wasannin ta na neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar 2021, tana mai zargin gwamnatin kasar da yin katsalandan a harkokin hukumar kwallon kafar kasar.

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika.
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika. © CAFOnline.com
Talla

A ranar 10 ga wannan watan na Maris da muke ciki ne ma’aikatar matasa da wasanni ta kasar Chadi ta rusa shugabancin hokumar kwallon kafar kasa, biyo bayan abin da ta kira rashin tafiyar da hukumar yadda ya kamata.

Hakan ya sa akwai yiwuwar hukumar kwallon kafa ta duniya ta dakatar da kasar ta Chadi.

Babu wani karin  bayani da aka samu daga CAF din ya zuwa yanzu.

A halin da ake ciki, Chadi ta riga ta fita daga jerin wadanda za su samu tikitin shiga gasar cin kofin na nahiyar Afrika da za ta gudana a Kamaru a  farkon shekara mai zuwa bayan da maki daya kawai ta samu daga wasanni hudun farko da ta buga na neman cancantar.

A gobe Laraba za su kara da Namibia, kana su yi tattaki zuwa Mali a karshen mako, kuma CAF ta tabbatar da cewa za ba abokan hamayyarsu kwallaye 3 da banza da maki 3 a kan Chadin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.