Isa ga babban shafi
Wasanni

Babu kocin da ya isa ya hanani buga gasar cin kofin Afirka - Adebayor

Tsohon fitaccen dan wasan gaba na kasar Togo, Emmanuel Adebayor, ya caccaki kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai kan yunkurin su na hana 'yan wasan Afirka buga gasar cin kofin nahiyar ta AFCON da za a fara cikin watan Janairu a Kamaru.

Emmanuel Adebayor lokacin da yana Real Madrid a Spain
Emmanuel Adebayor lokacin da yana Real Madrid a Spain REUTERS/Juan Medin
Talla

Yayin bayyana bacin ransa akan matakin kungiyoyin na Turai, Adebayor ya ce babu wani mai horas da 'yan wasa a duniya da ya isa ya hana shi wakiltar kasarsa domin buga gasar AFCON.

Tun bayan barkewar annobar Korona, kasashen Afirka da dama suka sami kansu cikin fafutukar ganin manyan taurarinsu sun wakilcesu wajen buga wasannin sada zumunta da wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022, sakamakon yadda kungiyoyin Turan da ‘yan wasan ke takawa leda, suke ta kokarin dakile balaguron da suke yi zuwa gida, musamman a kasashen da suke ganin sun fi fuskantar barazanar cutar ta Korona.

A cikin wasikar korafin da suka rubuta, kungiyoyin kwallon kafar Turan sun shaidawa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA cewar,  Kamaru ba za ta iya ba da tabbacin kare lafiyar taurarinsu daga kamuwa da cutar Korona ba, a yayin wasannin da za a fafata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.