Isa ga babban shafi
Wasanni

Napoli za ta hana 'yan wasanta wakiltar kasashensu a gasar AFCON

Rahotanni daga Italiya na cewa, kungiyar Napoli da ke gasar Seria A, na shirin daukar matakin shari'a kan kasashen da suka gayyaci ‘yan wasansu dake taka mata leda domin buga gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka ta AFCON, wadda ake sa ran farawa a watan Janairu.

Victor Osimhen, dan wasan gaba na kungiyar Napoli.
Victor Osimhen, dan wasan gaba na kungiyar Napoli. Filippo MONTEFORTE AFP/Archives
Talla

A ranar Talata ne dai, shugaban hukumar CAF Patrice Motsepe ya tabbatar da cewa gasar AFCON za ta gudana kamar yadda aka tsara ta, daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga Fabrairu da ke tafe a Kamaru, sabanin rahotannin da ke cewar akwai yiwuwar a dage gasar har zuwa watan Satumba.

Sai dai, daya daga cikin lauyoyin kungiyar Napoli Mattia Grassani, ya ce za su  dauki matakin shari’a don kare ‘yan wasan kungiyar, musamman ganin yadda cutar COVID-19 ta yi kamari a sassan duniya, kuma a Kamaru kashi 5 cikin 100 na yawan al’ummar kasar ne kawai aka yi wa alluran rigakafin annobar, abinda ya ce babbar hujja ce a gare su.

Kalidou Koulibaly mai tsaron baya na kungiyar Napoli
Kalidou Koulibaly mai tsaron baya na kungiyar Napoli Filippo MONTEFORTE AFP

Grassani ya ce Napoli ta kashe makudan kudade a kan ‘yan wasan ta dan haka ba za ta nade hannu tana kallo su kamu da cutar Korona yayin halartar gasar cin kofin kasashen Afirka ba.

Kungiyar Napoli dai ka iya rasa manyan ‘yan wasanta daga Nahiyar Afirka akalla guda biyar idan har za su wakilici kasashensu. ‘Yan wasan kuwa sun hada da  Adam Ounas, Kalidou Koulibaly, Faouzi Ghoulam, André Anguissa da kuma Victor Osimhen, dan wasan Najeriyar da a jiya ya ce zai iya halartar gasar, sakamakon murmurewar da yayi daga raunin da ya samu akansa a lokacin wani wasa da ya bugawa Napoli a cikin watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.