Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Salah na Masar ya koma Liverpool bayan shan kaye a gasar AFCON

Mohamed Salah na Masar ya isa sansanin ‘yan wasan kungiyarsa ta Liverpool a yau talata bayan kammala dokawa kasarsa wasannin cin kofin Afrika da suka sha kaye a wasan karshe hannun Senegal zakarar nahiyar.

Mohamed Salah na Masar bayan shan kaye a wasan karshe na gasar cin kofin Afrika.
Mohamed Salah na Masar bayan shan kaye a wasan karshe na gasar cin kofin Afrika. Charly TRIBALLEAU AFP
Talla

Salah wanda ya doka dukkanin wasannin Masar 7 karkashin gasar yana cikin ‘yan wasan Liverpool da za su kara da Lester City a alhamis mai zuwa bayan rashin ganinsa na wata guda saboda gasar ta AFCON da ta gudana a Kamaru.

A lahadin da ta gabata ne aka kammala gasar ta cin kofin Afrika inda Masar ta yi rashin nasara a bugun fenariti hannun Senegal inda Sadio Mane ya zurawa kasarsa kwallon da ta kaita g adage kofin na Afrika karon farko a tarihi.

Babu dai tabbacin lokacin da Mane zai koma Anfield dai dai lokacin da kasarsa ke ci gaba da shagulgulan dage kofin, koda ya ke mai horar da Liverpool Jurgen Klopp yayin wata zantawarsa gabanin doka wasan na karshe ya ce koma waye cikin ‘yan wasan nasa biyu ya dage kofin dole zai samu hutu zuwa laraba ko alhamis gabanin dawowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.