Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu tsuguno bata karewa Mane da Salah ba

Bayan karawar da suka yi a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka da aka kammala a kasar Kamaru, da alama dai tsuguno ba ta karewa taurarin kwallon kafar kasashen Masar da Senegal ba, wato Sadio Mane da kuma Muhammad Salah, la’akari da cewar nan gaba kadan za su sake fafatawa a wani fagen na dabam.

Sadio Mane da Mohammed Salah.
Sadio Mane da Mohammed Salah. AFP - DANIEL BELOUMOU OLOMO,KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Jadawalin wasannin neman cancanta ko tikitin halartar gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a kasar Qatar ya nuna cewar Masar da Senegal za su sake kece raini a cikin watan Maris, inda kowace kasa za ta yi tattaki zuwa gidan abokiyar hamayyarta.

A sauran wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya a Qatar, Ghana za ta kara da Najeriya, Kamaru da Algeria, Mali da Tunisia, sai kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da za ta fafata da Morocco.

Sai dai fafatawar da za a yi  tsakanin Masar da Senegal ake sa ran za ta fi daukar hankali, zsaboda fitattun 'yan wasan gasar Firimiyar Ingila Salah da kuma Mane.

A bangarensa Sadio Mane ba wai kawai ya taimakawa Senegal ta lashe kofin gasar Afirka a karon farko bane, ya kafa tarihin zama gwarzon dan wasan da ya fi fice a gasar ta AFCON.

Mane mai shekaru 29, ya zura kwallaye uku daga cikin 9 da Senegal ta ci a wasanni bakwan da ta buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.