Isa ga babban shafi
wasanni-Gasar cin kofin Afrika

CAF ta sauya wasannin cin kofin Afrika 2 daga Doula zuwa Yaounde

Hukumar CAF ta sanar da sauya wajen doka wasannin gasar cin kofin Afrika guda biyu daga filin wasa na Japoma da ke Doula zuwa filin wasa na Ahmadu Ahidjo da ke birnin Yaounde.

Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Patrice Motsepe.
Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika Patrice Motsepe. AP - Themba Hadebe
Talla

Wasu jami’an hukumar ta CAF da ke karin bayani kan dalilin sauya filayen wasannin sun ce matakin na da nasaba da rashin ingancin filin wasan na Douala biyo bayan turmutsutsun da ya hallaka mutane 8 dama yadda ‘yan wasa ke wahaltuwa.

Wasannin da aka sauyawa filin sun hada da guda daga matakin kwata final da kuma wasan gab da karshe a ranar 2 ga Fabarairu.

Tun a talatar da ta gabata, shugaban hukumar ta CAF Patrice Motsepe ya sanar da shirin dauke wasu wasannin daga  filin wasa na Olembe amma kuma ba a kai ga sanar da matakin ba sai bayan wani dogon taron masu ruwa da tsaki na hukumar a jiya laraba.

Sanarwar da CAF ta fitar ta ce wasan da aka tsara za su gudana a filin wasa na Olembe mai daukar mutane dubu 60 ba zai gudana ba har sai hukumar ta samu ingantaccen rahoton da ta bukata kan musabbabin turmutsutsun da ya kashe mutane.

Yanzu haka dai akwai wasan gab da karshe na ranar 3 ga Fabarairu da aka tsara zai gudana a filin wasan na Olembe kuma har zuwa yanzu ba a kai ga sauya mishi waje ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.