Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Zan yi duk mai yiwuwa don lashe kofin AFCON - Salah

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Masar Mohammed Salah ya sake jaddada kudirinsa na lashe gasar Afrika ta AFCON da ke gudana a kamaru.

Mohammed Salah, kyaftin na babbar tawagar kwallon kafar Masar.
Mohammed Salah, kyaftin na babbar tawagar kwallon kafar Masar. CHARLY TRIBALLEAU AFP
Talla

Shahararren dan wasan na Liverpool ya bayyana haka ne bayan doke Ivory coast da suka yi, lamarin da y ba su damar zuwa gasar daf da na kusa da karshe ta bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Masar za ta gwabza da Morocco a wasan quarter finals, kuma salah ya kagara ya jagoranci kasarsa zuwa ga nasara bayan da ta sha kashi a wasan karshe a shekarar 2021 a hannun Kamaru.

Salah ya ce kofin AFCON ne abin da yake matukar bukatar ya lashe, duk da cewa ya lashe kofin firimiyar Ingila da na zakarun nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.