Mane ya taimawa Senegal zuwa wasan karshe na AFCON a Kamaru
Kasar Senegal ta tsallaka zuwa matakin wasan karshe na gasar cin kofin Afrika da ke gudana a yanzu haka a kasar Kamaru, bayan ta lallasa Burkina Faso da kwallaye uku da 1 a fafatawar da suka yi daren Laraba a filin wasa na Ahmadu Ahidjo da ke birnin Yaounde.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:34
Abdou Diallo da Isrissa Gana Gueye da kuma Sadiyo Mane suka taimakawa tawagar Senegal zuwa matakin karo na biyu a jere, kuma na 10 a tarihinta.
Burkina Faso
‘Yan wasan Burkina Faso dai sun nuna kansu a matsayin matasa masu hazaka da kuma sha'awar sanya farin ciki ga magoya bayansu a kasar da ke cikin tashin hankali bayan hambarar da shugaba Roch Marc Christian Kabore a wani juyin mulkin da sojoji suka yi a makon jiya.
Lions Taranga
Tawagar Lions Taranga dake matsayi na daya a jadawalin FIFA wajen iya taka leda a Afirka, na jiran daya daga cikin kasashe biyu da zasu fafata anjima domin sanin da wa zata kara wasan karshe a ranar Lahadi, tsakanin Kamaru mai masaukin baki da kuma Masar wacce ba kanwar lasa ba ce a harkar tamola.
CAF
To, hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta sauya lokacin da ya kamata a doka wasan neman matsayi na uku na gasar cin kofin Afirka
CAF ta maido da lokacin ne zuwa ranar Asabar Mai zuwa tsakanin Burkina Faso da ko Masar ko Kamaru (za’a gane bayan wasansu na wannan Alhamis) maimakon Lahadi ranar da ake doka wasan karshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu