Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Ghana ta tabbatar da sallamar kocinta bayan ficewa daga AFCON

Ghana ta tabbatar da sallamar mai horar da ‘yan wasan babban tawagar kwallon kafarta, Milovan Rajevac biyo bayan rashin tabuka wani abu a gasar cin kofin nahiyar Afrika da ke gudana a kasar Kamaru, kuma yanzu ya zame mata dole ta hanzarta ta samu sabon koci da zai jagoranci tawagar a wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a ayi nan da watanni 2.

Milovan Rajevac, mai horar da 'yan wasan Blackstars ta kasar Ghana.
Milovan Rajevac, mai horar da 'yan wasan Blackstars ta kasar Ghana. Reuters
Talla

An sa ran za a sallami Rajevac bayan da Ghana ta fadi a hannun comoros da ci 3-2 a makon da ya gabata, lamarin da ya sa ta fice daga gasar duk da yadda ake kallonta a matsayin daya daga cikin manyan tawagogin gasar.

Ma’aikatar wasannin Ghana ce ta nemi a sallame shi, kwana guda bayan wasan da suka samu mummunan sakamako, amma sai a jiya Alhamis ne hukumar kwallon kafar kasar ta tabbatar da haka bayan taron da ta yi a ranar Laraba.

Watanni 4 ne kacal Rajevac mai shekaru 68 ya yi a tawagar bayan da ya dawo a karo na 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.