Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Comoros ta fitar da Ghana daga gasar cin kofin Afrika a Kamaru

Comoros ta yi waje da Ghana daga gasar cin kofin Afrika bayan lallasa ta da kwallaye 3 da 2 a karawarsu ta jiya talata, wadda Ghanar ta karkare da ‘yan wasa 10 bayan bai wa Andre Ayew jan kati.

'Yan wasan Comoros bayan nasarar tsallakawa zagayen kasashe 16 a gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Kamaru.
'Yan wasan Comoros bayan nasarar tsallakawa zagayen kasashe 16 a gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Kamaru. Daniel BELOUMOU OLOMO AFP
Talla

Rabon Ghana da ficewa daga gasar cin kofin Afrika a matakin rukuni tun a shekarar 2006 yayinda kuma rabonta da kai kofin gasar gida tun 1982 ko da ya ke ta kai wasan karshe a gasar Nations League ta 2010.

Comoros wadda yanzu ke matsayin ta 132 a jadawalin FIFA iya tsallakawa matakin gaba na gasar ta cin kofin Afrika na matsayin gagarumar nasara kuma bazata a gareta.

Yanzu haka Comoros ta koma matsayin ta 3 ne a rukuninta na C kasa da Morocco da kuma Gabon bayan rashin nasara a wasanni 2 da ta doka a Kamarun.

Kankanuwar kasar da ke da matukar rauni a kwallo, ta samu tikitin iya shiga gasar ta cin kofin Afrika ne karon farko a 2016 bayan yunkuri har sau 20.

Ficewar Ghana daga gasar zai kara zama matsin lamba ga mai horarwa Milovan Rajevac wanda ya fara sabon wa’adi a watan Satumban da ya gabata bayan karewar kwantiraginsa na farko.

Yanzu haka Ghana za ta koma gida don shirye-shiryen tunkarar wasan cike gurbin da zai bata damar samun tikiti a gasar cin kofin Duniya, wasan da za ta kara da ko dai Najeriya ko Senegal ko Morocoo ko kuma Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.