Ghana na fuskantar barazanar ficewa daga gasar cin kofin Afrika
Ghana na shirin karawa da Comoros yau talata, a karkashin gasar cin kofin Afrika da ke ci gaba da gudana a Kamaru, wasan da ke matsayin babban kalubale ga kasar ta yammacin Afrika domin kuwa matukar ta na son ci gaba da kasancewa cikin gasar dole ta yi nasara a wasan.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka tawagar ta Black Stars ke matsayin ta 3 a rukuninta na C bayan samun maki 1 tal a wasanninta 2 da ta doka bayan da ake zura mata kwallon kurarren lokaci a dukkanin karawarta biyu .
Karawar Ghana ta farko dai ta yi rashin nasara hannun Morocco da kwallo 1 mai ban haushi kwallon da aka zura mata a minti na 83 gab da Karkare wasa, yayinda ta tashi wasa kwallo 1 da 1 tsakaninta da gabon shima dai wannan karawa a farko Ghanar ke jagoranci har zuwa minti na 88 gabanin Jim Allevinah na Gabon ya zura mata kwallo mai cike da bajinta.
Da misalin karfe 9 na daren yau wasan zai fara wanda idan har bata yi nasara ba kai tsaye za ta fice daga gasar.
Morocco dai ke jagorancin rukunin na C da maki 6 bayan nasara a dukkanin wasanninta biyu biye da Gabon mai maki 4 bayan nasara a wasa 1 canjaras a wasa daya, kuma suma dai kasashen biyu wato jagora da mai bi mata Morocco da Gabon kenan nada wasa a yau ko da ya ke ma tuni aka fara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu