Isa ga babban shafi
Kamaru - kwallon kafa

CAF ta dora alhakin iftila'in Yaounde kan rashin bude kofofin shiga fili

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Afrika Patrice Motsepe yace babu dalilin rufe kofofin filin wasan Kamaru da aka yi, abinda ya kaiga tirmitsistin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 8 kafin karawar Kamaru a gasar cin kofin Afirka dake gudana.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Afirka Patrice Motsepe, yayin jawabi kan tirmutsitsi da ya hallaka mutane a filin wasan Olembe dake Yaounde babban birnin kasar Kamaru, 24/01/2022
Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Afirka Patrice Motsepe, yayin jawabi kan tirmutsitsi da ya hallaka mutane a filin wasan Olembe dake Yaounde babban birnin kasar Kamaru, 24/01/2022 AP - Themba Hadebe
Talla

Yayin ganawa da manema labarai, Motsepe yace ya dace a bude kofofin shiga filin wasan domin baiwa jama’a damar amfani da su, yayin da yace an kaddamar da bincike domin gano abinda ya haifar da matsalar.

Rahotanni sun ce mutane 8 ne suka mutu, yayin da wasu 38 suka samu raunuka lokacin da mutane suke kokarin shiga filin wasan Olembe domin kallon karawar Kamaru da Komoros.

Binciken farko yace daga cikin mutane 8 da suka mutu akwai mata 2 dake da shekaru 30 da kuma yaro guda, yayin da wani jaririn da hadarin ya ritsa da shi ke asibiti inda yake samun kula daga likitoci.

Ministan sadarwar kasar Rene Emmanuel Sadi yace daga cikin mutane 38 da suka jikkata, guda 7 na cikin mawuyacin hali.

Motsepe ya bukaci gudanar da bincike bayan shugaba Paul Biya ya bada umurnin domin gano abinda ya haddasa hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.