Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Comoros za ta sadaukar da dan wasa 1 don tsare mata raga a wasansu da Kamaru

Da yiwuwar Comoros za ta sadaukar da dan wasanta 1 don tsare mata raga a karawarsu ta yau litinin da Kamaru mai masaukin baki a gasar cin kofin Afrika, sakamakon yadda ‘yan wasanta 12 ciki har da masu tsaron raga biyu suka harbu da covid-19.

Tawagar 'yan wasan Comoros a Kamaru.
Tawagar 'yan wasan Comoros a Kamaru. REUTERS - MOHAMED ABD EL GHANY
Talla

A cewar mai horar da masu tsaron raga na tawagar ta Comoros Jean-Daniel Padovani harbuwa da Moyadh Husseini da kuma Ali Ahmada suka yi da corona kari kan rashin lafiyar Selim Ben Boina ya bar tawagar kasar ba tare da mai tsaron raga ba.

Padovani ya ce har zuwa yanzu basu kammala tantance dan wasan da za su sadaukar don tsare musu ragar ba.

Comoros wadda ta yi sa’ar tsallakawa matakin tawagogi 16 a karon farko na da jumullar ‘yan wasa 12 ne da suka harbu da corona kuma bisa sahalewar AFCON idan har kasa na da ‘yan wasa 11 kai tsaye za ta shiga karawa ko da bata da mai tsaron raga.

A taron manema labaran da Comoros ta yi jiya gabanin karawar ta yau, dan wasanta na tsakiya Nadjim Abdou ya amsa cewa tabbas tawagarsa na laluben mai staron raga a tsakankanin ‘yan wasa amma yasan tabbas ba zai zama shi ba.

Acewar Abdou koda yaushe yakan rike tsakiya ne, amma a shirye yake idan ya zama dole ya tsare raga zai sadaukar domin kasarsa, Comoros dai ta bayar da mamakin kaiwa wannan mataki ne bayan doke Ghana da kwallaye 3 da 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.